LABARI MAI DADI: Sojoji Sun Sheke Rikakken Dan Ta’addan Da Ya Addabi Yankin Katsina Da Zamfara, Mai Sun Dangote Zuwa Barzahu

0

Rundunar sojojin Nijeriya ta bayyana cewa jami’an ta sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan a dazukan jihohin Katsina da Zamfara.

Kakakin rundunar tsaron Nijeriya Mejo Janar John Enenche a yau Lahadi ya kara da cewa dan ta’addan dajin nan da ya shahara a dazukan jihar Katsina da Zamfara da Arewacin Nijeriya mai suna Dangote an kashe shi a wani hari da jami’an soji suka kaiwa dabarsa’.

Ya kara da cewa Sojojin saman sun halaka shi da wasu mahara da dama sun halaka sakamakon bayyanan sirri da rundunar ta samu a ranar Alhamis. shafin rariya na ruwaito wannan labari.

source https://www.hausaloaded.com/2020/07/labari-mai-dadi-sojoji-sun-sheke.html

Leave A Reply

Your email address will not be published.