Jagoran Musulmi Duniya Sheikh Recep Tayyip Erdogan Yana Fuskantar Barazana ~ Datti Assalafy

0

Yanzu a duniya babu wani jagora da yake magana akan hakkin Musulunci da Musulmai kamar shugaban Kasar Turkiyyah Sheikh Recep Tayyip Erdogan mujaddadin Daular Musulunci ta Usmaniyyah, bayan ya ‘yanto Masallacin Hagia Sophia yanzu hankalinshi ya koma Masallacin Qudus

Hakika taron dangin yahudu da nasara ba zasu taba kyaleshi ba, domin yayi abinda babu wani Musulmi shugaba a duniya da yayi irinsa shekaru 500 da suka gabata, suna ganinshi a matsayin babban barazana da ya kamata a kawar dashi ta kowace irin hanya

Ina ji a jikina kamar shugaba Recep Tayyip Erdogan ba zai jima ba zasu kawar dashi, shi kadai ya rage yanzu cikin shugabanni Musulmai masu tsananin kishin Musulunci

Ina jin tsoron yahudawa zasu kifar da gwamnatinsa ta hanyar juyin mulkin sojoji wanda suka taba yunkurin haka shekaru 2 da suka gabata, duk wanda ya san makircinsu ya san tabbataccen al’amari ne ba zasu taba kyaleshi ba har sai sun ga baya numfashi

Kuma duk wannan kokari da shugaba Erdogan yake yiwa Musulunci a duniya akwai wasu shugabannin kasashen Musulmi da basa son shi, kuma basa goyon bayanshi saboda tsoro suna ganin yana taba ra’ayin uwayen gidansu turawa

Yaa Allah Ka kareshi, Ka tsareshi, Ka cika masa burinsa na dawo da martaban Daular Usmaniyyah
Yaa Allah Ka haramtawa makiyan Musulunci samun nasara a kanshi
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

source https://www.hausaloaded.com/2020/07/jagoran-musulmi-duniya-sheikh-recep.html

Leave A Reply

Your email address will not be published.