Bireziyar ‘a cuci maza’ na sanya cutar daji – Dr Habiba Ismail

0

‘Push up bra’ shi ne sunan da ake kiran bireziyar da ake wa lakabi da ‘a cuci maza’.

Kwarrariyar likita a asibitin Spacialist dake jihar Bauchi, Dr Habiba Ismail, tayi kira ga  mata da su guji irin wannan rigar mama da ke hana jini ratsa jiki.

Dr Habiba tayi wannan kira ne lokacin da take zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya ‘NAN’ a jihar Bauchi.

Ta kara da cewa “wannan bireziyar da yanzu ake yayi tana dauke da wani karfe da ke hana jini ya zagaya a sassan jikin dan dam.”

Dr ta ce “rashin ratsawar jini sassan jikin yana saka ‘ailment’ wanda dangi ne na cututtukan mama da suke kawo cutar daji.”

source https://www.hausaloaded.com/2020/07/bireziyar-cuci-maza-na-sanya-cutar-daji.html

Leave A Reply

Your email address will not be published.