An zargi hukumar soji da neman iyalan sojojin da aka kashe a Katsina su bada kudin motar da za’a kai gawarsu gida da kuma Makara

0

A makon daya gabata ne mutanen jihar Katsina suka shiga halin fargaba bana  da Bam ya tashi ya kashe yara kusan 7, sannan kuma wasu suka kashe sojoji kusan 20.hutudole na ruwaito

Wani dan Jarida Fisayo Soyombo wanda ya shahara sosai wajan kawo ingantattun Labarai, shine ya fara bayyana mutuwar tsohon gwamnan Oyo, Surukin gwamnan Kano, Abiola Ajimobi amma daga baya Iyalai da wasu na kusa da mamacin suka karyatashi, amma daga baya kuma suka tabbatar da ya mutu.
A wannan karin Soyombo ya kwarmata ta shafinsa na sada zumunta cewa Hukumar sojin ta nemi iyalan sojojin da aka kashe a Katsina da su bayar da kudin mota sannan su bayar da makarar da za’a saka mamatan a ciki a kaisu mahaifarsu inda za’a binne.

Yace za’a dauki gawar wakinne daga Asibitin sojoji na 44 dake Kaduna amma yace bai kamata a sakawa jaruman da suka mutuwa kasar su da irin wannan abuba, ya kamata a binnesu cikin mutumci. 

source https://www.hausaloaded.com/2020/07/an-zargi-hukumar-soji-da-neman-iyalan.html

Leave A Reply

Your email address will not be published.